Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Ya yi Murabus

0
234

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Abdulaziz Garba Gafasa ya yi murabus daga mukaminsa.

A wata wasikar ajiye aiki da jaridar PRIME TIME NEWS, ta samu, Gafasa ya ce ya yi murabus ne bisa dalilai na kashin kai.

Jaridar Daily News 24 ta rawaito cewa, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Doguwa, Alhaji Salisu Ibrahim Riruwai ya tabbatar da murabus din shugaban majalisar.

Dan majalisar ya ce ” wasikar murabus din shugaban majalisar bisa kashin kansa an aikara majalisa da misalin karfe 1:08 na dare”.

Wata Wasikar kuma ta tabbatar da cewa, shugaban masu rinjaye na majalisar, Kabiru Hassan Dashi shi ma ya ajiye mukaminsa sai dai ba a bayyana dalilan ajiyewar tasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here