Yanzu-Yanzu: Hukumar NCC Ta Bada Umarnin Rufe Layukan Wayar da Basu da Lambar Katin Dan Kasa

0
258

Hukumar kula da sadarwa ta kasa(NCC) ta bada wa’adin mako biyu ga kamfanunuwan sadarwa dake kasarnan da su rufe kowanne layin waya da bai yi rijistar katin dan kasa ba.

A sanarwar da hukumar ta fitar a yau Talata ta bakin daraktan hulda da jama’a na hukimar, Dr. Ikechukwu Adinde, ta bayyana cewa duk kamfanin sadarwar da yaki bin wannan umarni za a kwace lasisinsa.

Sanarwar ta ce “Kamfanunuwan waya su nemi dukkan masu amfami da layukan waya su sanya lambarsu ta jikin katin dan kasa wato(NIN).

“Masu amfani da layukan waya za su fara kai lambobinsu na katin dan kasa daga gobe 16 ga watan Disamba zuwa 30 ga watan Disamba.

” Bayan cikar wa’adin, duk wani layi da bashi da lambar katin dan kasa za’a rufe shi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here