Hamisu Chidari Na Shirin Zama Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano

0
165

Komai ya kammalu domin zabar dan majalisa mai wakiltar karamar Makoda, Hamisu Chidari a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin jihar Kano kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Matakin zaben Chidari a yau Talata ya biyo bayan murabus din da Abdul’aziz Gafasa tare da mataimakinsa suka yi da kuma shugaban masu rinjaye.

Sannan kuma rahotanni sun bayyana cewa, Majalisar za ta zabi Zubairu Hamza Masu dan majalisa mai wakiltar Sumaila a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Haka kuma anasaran yan majalisar za su zabi Labaran Madari mai wakiltar Warawa a matsayin shugaban masu rinjaye.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, a cikin dare yan majalisa 35 cikin 40 sun sanya hannu domin tsige shugaban majalisar da shugaban masu rinjaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here