Dalilan Da Yasa Na Sauke Sanusi Daga Sarautar Sarkin Kano – Ganduje

0
323

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a yau Talata ya bayyana dalilan da yasa ya sauke Malam Muhammadu Sanusi II daga mukamin Sarkin Kano.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne don ceto masarautun gargajiya daga cin zarafi.

Ganduje na jawabi ne a taron kaddamar da littafin rayuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan wamda dan jarida Bonaventure Philips Melah ya wallafa.

Gwamnan ya ce, Sanusi bai chan-chan ci zama Sarki ba a lokacin da aka nada shi a shekarar 2014, inda ya ce an nada tsohon Sarkin ne don batawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan rai.

A watan Afrilu na shekarar 2014 ne, a ka sauke Sanusi daga gwamnan babban bankin Najeria CBN bayan zargin da yayiwa wasu jami’an gwamnatin Jonathan da sace kudi Dala Biliyan 49.

A ranar 9 ga watan Maris ne dai Ganduje ya sauke Sanusi daga sarautar Kano.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ne ya nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here