Korona Zagaye na Biyu: El-Rufai Ya Bada Umarnin Rufe Makarantu

0
192

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bada umarnin rufe makarantu gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar daga ranar 16 ga watan Disamba, yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar Korona.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Muhammad ya fitar a yau Laraba.

“Ma’aikatar ilimi na sanar da al’umma, iyaye da dalibai sabuwar ranar rufe makarantu sakamakon samun yawaitar masu kamuwa da cutar Korona a jihar, wanda yake nuna cewa anfi samun wadanda ke kamuwa da cutar a karo na biyu”.

Sanarwa ta kara da cewa “ma’aikatar lafiya ta jihar, ta tabbatar da cewa zagaye na biyu na cutar yafi shafar yan shekaru 10 zuwa 35 wadanda yawanncinsu suna fannin ilimi”

Daga karshe sanarwar ta ce dole ne a kammala dukkan wata jarrabawa a ranar ko kafin ranar 15 ga watan Disamba a dukkan makarantun jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here