An yi Kira Ga Ƴan Mata da su Kaucewa Ɗabi’ar Shan Miyagun Kwayoyi

0
311

 

 

 

 

Daga Abdulwahab Idris Sulaiman

Kungiyar wayar da kan mata akan ilar shaye-shaye wato Network for Women Awareness on Drugs Abuse, kungiya ce da aka kafa kusan shekaru uku da suka gabata,Kuma tunda aka kafa kungiyar take fafutaka wanjan wayar da kan mata akan ilar shaye-shaye da Kuma ilar da hakan ke haifarwa ga lafiyar jikin Dan Adam.

A zantawar wakilinmu da shugabar kungiyar Hajiya Rabi Yarima ta bayyana Mana irin hanyoyin da su ke bi domin magance Wannan dabi’ar ta shaye-shaye a cikin Mata in da ta ce suna zuwa Asubitoci, Makarantun Sakandire hadi da Makarantun gaba da Sakandire ,Taron Biki,Suna da duk wani waje Wanda Mata su ke taruwa.

Sannan ta kara da cewa wani lokacin ma suna Kama wajen taruka domin gayyatar Mata masu shaye-shaye Hadi da Wanda basayi domin dai duk a gudu tare a tsira tare.

Rabi Yarima ta Kara da cewa nasarorin da suke samu Ba za su lissafu ba, musanmanma a guraren da ta bayyana in da ta ce hakan su na cinma Ruwa.

Bugu da kari ta ce kunsan Suma Yan Kungiyar Malaman lafiya ne Hadi da Malaman Makarantu kuma ko a gun aikin su suna nunawa Mata ilar Wannan dabi’ar ta shaye-shaye da Kuma ilar take haifarwa.

A karshe dai ta yi Kira ga al’umma da su bada gudunmawar su domin kawo karshen Wannan Dabi’ar, in da Kuma takara da jan hankalin jama’a da su guji shiga Wannan dabi’a ta shaye-shaye musanmanma ya’ya Mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here