Ƴan Daba Sun Tarwatsa Taron Da Aka Shirya Kan Matsalolin Tsaro a Arewacin Najeriya

0
506

Yan daba dauke da makamai, a yau Litinin, sun dira wajen taron duba yanayin matsalar tsaro da Arewacin Najeriya ke fuskanta da gammayar kungiyoyin Arewa ta CNG ta shirya a Kaduna.

Taron wanda aka shirya fara shi da karfe 11 na safe zai mayar da hankali ne wajen samar da hanyoyin da al’umma za su bi don kare kansu, tare da tabbatar da hadin kai tsakanin jihohin Arewacin Najeriya 19.

Fara taron ke da wuya yan daban suka dinga fitowa da ashana da sauran makamai na tayar da wuta wanda hakan ya tilasta mahalarta taron da masu ruwa da tsaki fara guduwa don tsira da ransu. Yan daban sun lalata abubuwa a wajen.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, mahalarta taron da suka hada da masana kan fannin tsaro, shugabannin addini da sarakunan gargajiya da kungiyoyi sun tsere don kula da lafiyarsu bisa tsoron kai musu hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here