Shugaban Kwamitin Yaki da Korona, Boss Mustapha Ya Killace Kansa

0
117

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da annobar Korona na fadar shugaban kasa, Boss Mustpha ya killace kansa bayan iyalansa sun kamu da cutar Korona.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, 13 ga watan Disamba, Boss Mustapha ya bayyana cewa:
“Ina sanar da al’umma cewa, wasu daga iyalan gidana sun kamu da cutar Korona a yammacin jiya. An killace su a daya daga cikin cibiyoyin gwamnati inda su ke karbar kulawa.

” Ni da matata, gwaji ya nuna bama dauke da cutar, amma za mu ci gaba da killace kanmu tare da yin aiki daga gida kamar yadda jami’an lafiya suka bada shawara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here