Manyan Jami’an Sojin Najeriya 18 Sun Kamu da Cutar Korona

0
219

Wata majiya a rundunar sojan Najeriya ta shaidawa gidan talabinin na Channels cewa, Janar-Janar na Soji 18 ne su ka kamu da cutar Korona.

Manyan jami’an sojan sun kamu da cutar ne daga marigayi Manjo Janar Olu Irefin wanda ya rasa ransa sakamakon cutar ta Korona.

Majiyar ta ce, manyan jami’an sojin da suka kamu da cutar suna daga cikin wadanda suka halarci taron shekara babban hafsan soji a cibiyar rundudnar sojan dake Abuja.

An rawaito cewa, Janar Irefin ya ziyarci wasu abokan aikinsa a gida kafin ya halarci taron.

Haka kuma, hukunar dakile yaduwar cutuka ta NCDC ta bada umarni ga wadanda suka halarci taron tare da matayensu da su killace kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here