Yanzu-Yanzu: Gwamna Masari Ya Bada Umarnin Rufe Makarantun Kwana a Jihar Katsina

0
141

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari , ya bada umarnin a gaggauta rufe makarantun kwana a jihar don kare su daga harin yan bindiga.

Umarnin gwamnan na zuwa ne bayan harin baya-bayan nan da aka kai makarantar Kankara inda ake fargabar an sace daruruwan dalibai.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Masari ya tabbatar da cewa, an tura sojoji yankin da abun ya faru inda yanzu haka suke kokarin kubutar da daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here