Ana Fargabar An Sace Ɗalibai 600 Bayan Harin da Ƴan Bindiga Su ka kai wata Makaranta a Katsina

0
483

A kalla dalibai 600 cikin 800 na makarantar GSS Kankara dake jihar Katsina suka bace bayan harin da yan bingida suka kai makarantar a daren jiya Juma’a.

Jaridar Dailiy Nigerian ta rawaito cewa garin na Kankara ya shafe shekaru yana fama da matsalar garkuwa da mutane da aikin yan bindiga.

Wani malamamin makarantar da ya nemi a boye sunansa ya bayyanawa jaridar cewa, yan bindigar sun kai harin da karfe 9:30 na dare.

Ya ce yan bindigar sun fara harbi kan iska ne wanda ya sanya firgici da rudewa kafin su balla kofar makarantar.

Ya ce makarantar tana da dalibai 800 banda yan JS3 da SS3 wadanda yanzu basa makaranta.

Ya kara da cewa, dalibai 600 har yanzu basu dawo makarantar ba awanni bayan kai harin. “Har yanzu muna fatan wasu daga cikinsu sun gudu zuwa daji ne”, inji shi.

Malamin ya ce bayan yan bindigar sun tattara daliban a waje guda, sun kai su zuwa kauyen Pauwa, inda suka ajiye baburansu.

Yayin tattaunawa da gidan rediyon BBC, Kakakin rundunar yan sanda na jihar Katsina, DSP Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami’ansu sun ji raunika yayin artabu da yan bindigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here