An yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Wajen Kawo Mafita Kan Yawaitar Sace Mutane da Kashe-Kashe a Arewa

0
173

 

Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe ( Grassroot Care & Aid Foundation ) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo mafita na sace-sace da asarar rayuka a Sakamakon abubuwan da suke faruwa a bangaren tsaro.

Shugaban Gidauniyar,  Amb Auwalu Muhd Danlarabawa shi ne yayi kiran Jim kadan bayan samun rahoton kwashe dalibai a makaranta a garin Kankara dake jihar Katsina, inda ya ce babu wani uzuri ko sassauci ya Zama wajibi a fadawa gwamnati gaskiya, da ta yi duba kan irin wadannan matsalolin tsaro da suke cigaba da lakume rayukan al’umma babu gaira babu dalili ba dare ba rana.

Kazali Amb Auwal Danlarabawa ya ce nauyi ne akan duk wata kungiya da ta daukarwa kan ta gwagwarmayar tabbatar da cigaban al’umma ta fito haikan domin ganin gwamnati ta dauki mataki akan halin da alumma suka tsinci kansu na rashin kwanciyar hankali da nakasu a bangaren tsaro tare kisan kiyashin da ake wa wasu al’ummomi a sassan kasar nan.

Danlarabawa, ya ce dole ne bangaren zartaswa da kuma bangaren majalisa da shari’ah da ma Yan jaridu su mike tsaye domin ganin anyi maganin wannan matsalar da gaggawa domin su Allah ya bawa nauyin jan ragamar al’umma da kuma kare rayukan su da dukiyoyin su.

Haka zalika ya ce dole ne idan wadannan bangarori suka kasa cika amanar da aka dora musu su sauka su mika ragama ga rukunin mutanen da zasu iya duba ga ba yau aka fara shiga wannan yanayi ba, kuma har yanzu lamarin karuwa yake ta ko’ina.

Daga karshe yayi kira ga daukacin al’umma dasu dukufa da adduo’i ba dare ba rana a gidaje, Masallatai, majami’oi, da makarantu, tare da komawa zuwa ga Allah don ganin an samu damar kawo karshen wadannan musifu dake afkuwa a arewacin kasar nan Wanda kowa ke Kuka dashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here