Yanzu-Yanzu: An Sake Kama Faisal Maina

0
158

An sake kama Faisal Maina, wanda da ne ga tsohon shugaban kwamitin asusun yan fansho na fadar shugaban kasa, Abdulrasheed Maina.

Kamashin na zuwa ne mako guda bayan an sake kama mahaifinsa wanda ya gudu zuwa kasar Nijar bisa gujewa tuhumar da ake yi masa ta badakalar kudi Naira Biliyan 2 a kotun tarayya dake Abuja.

Faisal wanda ake tuhuma da laifuka uku mabanbanta dangane da badakalar kudi a kotun, ya tsallake belin da aka bashi tare da dena halartar zaman kotun.

Mai shari’a Okon Abang a ranar 24 ga watan Nuwamba ya soke belin nasa tare da bada umarnin a kama shi.

Haka kuma alkalin ya umarci wanda ya tsayawa Faisal, wanda dan majalisar tarayya ne dake wakiltar kananan hukumomin Kaura-Namoda, Umar Dan Galadima da ya bayyana gaban kotun.

Sai dai yayin dawowa zaman sauraron karar a yau Alhamis, Lauyan wanda ya tsayawa Faisal, Mista M.E Sherif, ya bukaci kotun ta dakatar da sauraron karar kan batun don ya samu labarin cewa an kama Faisal.

“Mai Shari’a, na samu labari daga majiya mai tushe cewa an kama wanda ake tuhuma. An kama shi ne a daren jiya yanzu haka yana tsare”, inji Lauyan.

Lauyan hukumar EFCC, Malam Faruk Abdullahi, ya tabbatar da lamarin sai dai ya ce ba’a mika Faisal ga hukumar EFCC ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here