Wasanni: Zidane zai bar Real Madrid

0
112

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa, Zinedine Zidane ya shirya tsaf don yin hannun riga da Real Madrid a karshen wannan kaka da muke ciki duba da yadda yake ganin yanayin al’amura a kungiyar babu tabbas.

Rahotanni dai na cewa Zidane ya bukaci hukumomin kungiyar su sayo mai ‘yan wasa da suka hada da Pogba, Sadio Mane da Eduardo Camavinga, amma maimakon haka suka bar shi da ‘yan wasan da ba sa iya rawar gaban hantsi.

Mujallar Dariogol da ake wallafawa a kasar Spain ta ruwaito cewa Zidane zai yi hannun riga da Bernabeu a karshen wannan kaka a matsayin sakamakon tattaunawar fahimtar juna da suka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here