Korona: Da Yuwuwar Mu Kara Sanya Dokar Kulle a Kaduna – El-Rufai

0
166

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana damuwa bisa samun yawaitar masu kamuwa da cutar Korona sannan ya yi barazanr kara sanya dokar kulle a jihar idan mazauna jihar suka ci gaba da bijirewa matakan kariya daga cutar..

 

Gwamman jihar wanda ya sanar da hakan yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2021 a gidan gwamnatin jihar Kaduna ya yi nuni da cewa, jihar na samun karuwar masu kamuwa da cutar a yan makwannin nan wanda hakan yasa aka yanke shawarar cewa, duk wani ma’aikacin gwamnati sai anyi masa gwajin cutar.

Gwamna El-Rufai ya kuma roki mazauna jihar da su kaucewa taron jama’a, inda ya yi bayanin cewa cutar Korona gaskiya ce, sannan kotun tafi da gidanka za ta dawo da tilastawa mutane amfani safar rufe hanci da baki don hana yaduwar cutar.

Yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin, Malam Nasiru El-Rufai ya ce jihar Kaduna a shekaru 5 da suka wuce ita ce jiha ta daya tilo a kasarnan dake aiwatar da tsarin sabon kasafi a watan farko na Janairu sakamakon himmatuwar yan majalisar dokokin jihar.

A bangare guda kuma, kamfanin Bua ya bada tallafin motocin daukar marasa lafiya guda 3 da safar rufe hanci da baki guda dubu 50 ga gwamnatin jihar ta Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here