Ƙura ta lafa a kasuwar Dabbobi dake Uyo bayan da Naira 200 ta Haddasa Rikici

0
137

 

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Halin yanzu kura ta lafa a Wani rikici tsakanin Yan kasuwa biyu da Naira 200 ta haddasa ranar Laraba.

Majiyar labarin mu ta shaida mana cewa a kasuwar Dabbobi ta mayankar Uyo da akafi Sani da Suna sulota ne tsakanin Wani Dan asalin jihar da Kuma Wani Dan Arewa rikicin ya Fara lokacin da shi Dan asalin jihar yazo karbar cikon kudinsa naira 200 lamarin da ya jawo musu tayar da jijiyar wuya har yakai fada ya kaure tsakanin su lamarin da ya jawo raunata mutum biyar biyu da raunuka su sukayi dama an kaisu asibiti an musu jinya sun dawo gida yayin da sauran uku Kuma Suma aka sallame su.

Alhaji Muhammadu Bello ya shaidawa manema labarai cewa “Kura ta lafa mun koma harkokin mu kamar yadda aka saba”,  injishi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here