Za mu Rufe Jami’o’i Masu Zaman Kansu Matukar ASUU Ba Ta Janye Yajin Aiki Ba -NANS

0
109

Sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya ta NANS, Sunday Asefon, ya sha alwashin rufe jami’i’o masu zaman kansu a kasarnan matukar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke yi ya ci gaba.

Shugaban daliban na fadin hakan ne yayin tattaunawa da jaridar PUNCH a yau Laraba.

Ya yi ikirarin cewa yajin aikin da ASUU ke yi a halin yanzu shi ne mafi dadewa da aka taba yi.

Ya ce kungiyar Dalibai ta NANS za ta tattauna da wakilan gwamnati da shugabannin kungiyar ASUU don shawo kan matsalar yajin aikin.

Shugaban ya ce bayan tuntubar da za su yi tsakanin bangarorin biyu, kuma aka gaza samun matsaya, kungiyar daliban za ta rufe dukkan manyan makarantun kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here