NCC Ta Bada Umarnin Dakatar Da Yin Rijista Tare da Siyar da Sabon Layin Waya

0
184

Hukumar kula da sadarwa ta kasa NCC ta bada umarni ga kamfanunuwan wayoyi kan su dakata da siyar da sabon layin waya tare da yin rijista don bada dama wajen sake yin duba kan bayanan wadanda aka yiwa rijista.

Babban Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta NCC, Dr. Ikechekwu Adinde, a wata sanarwar da ya fitar yau Laraba ya ce ya zama dole kamfanuwan waya su bi wannan umarni har zuwa lokacin da za’a kammala binciken.

Ya ce, ministan Sadarwa Dr. Isa Pantami, ne ya bada umarni ga hukumar na ta fara gudanar da bincike kan tsarin yin rijista ga masu amfani da layukan waya.

Ya kuma yi gargadin cewa, rashin bin wannan umarni zai iya sa a dakatar da kamfani ko kuma a janye masa lasisin yin aiki.

Adinde ya ce binciken zai taimaka wajen gano nasarar da aka samu a yiwa layukan waya rijista.

Sannan yace umarnin ya zama dole bisa samun yadda ake amfani da layuka marasa rijista wajen aikata laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here