Nan kusa za mu bude Kan Iyakokin Najeriya -Buhari

0
149

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasarnan za ta bude kan iyakokinta nan kusa bayan sun kasance a rufe fiye da shekara guda.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a yayin wani taro da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulkin kasar da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata.

Buhari ya nanata cewa, dakile safarar makamai da muggan kwayoyi daga kasashe makwabta, na cikin dalilan rufe kan iyakokin.

Shugaban ya ce, tun da kasashen makwabtan Najeriya sun fahimci sakon da ke tattare da rufe iyakokin, yanzu haka akwai yiwuwar sake bude su nan kusa.

Tun a watan jiya ne, gwamnatin Najeriya ta bayyana kudirinta na sake bude kan iyakokin a daidai lokacin da farashin kayayyakin abinci ya tashi sama, gami da kiraye-kirayen da jama’a ke yi don ganin an budbude kamar yadda sashin Hausa na RFI ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here