Mayar Da Triumph, Gidan Zoo, Daula Hotel Da Masallacin idi zuwa Wajen Harkokin Kasuwanci Yana bisa Tsarin Doka -Kwamitin Majalisa

0
618

 

Shugaban kwamitin harkokin kasa na majalisar dokokin jahar Kano Hon. Muhammad Uba Gurjiya ya ce gwamnatin Kano ta hada gwiwa da ‘yan kasuwa domin mayar da kamfanin Triumph da Hotel din Daula da Gidan Zoo da masallacin idi zuwa wuraren kasuwanci amma ba sayarwa ta yi dungurungun ba.

Hon. Muhamamad Uba Gurjiya ya bayyana haka ne a cikin shirin Fitila Mai Haska Duhu na Radio Kano da aka gudanar a ranar Larabar nan.

Shugaban kwamitin Wanda shi ne wakilin karamar hukumar Bunkure a majalisar ya ce dukkanin gwamnatocin da suka gabata sun sayarwa da ma’aikata gidajen gwamnati haka kuma wasu ‘yan kasuwa ma ta mallaka musu wasu kadarorinta domin yin abin da zai amfani jama’a ba a wannan gwamnati aka fara irin haka ba, a yayin da kuma ta kulla yarjejeniya da wasu akan kadarorinta da suka shafi kasa.

Ya bayyana cewa mayar da wuraren zuwa wajen kasuwanci zai taimaka wajen kara farfado da tattalin arzikin jahar kano da kuma kare rayuka daga barazanar Namun daji.

Shugaban kwamitin kasa na majalisar ya kara da cewa bisa tanadin doka dukkanin al’amuran kasa gwamnatin jaha ce take da cikakken iko akai ko da kuwa gada ko saya aka yi za ta iya Karba don yin abin da zai shafi ci gaban jama’a.

Hon. Muhammad Uba Gurjiya ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta yi kokari wajen mayar da diyyar fili zuwa kaso 50% a madadin 40% a duk lokacin da ta karba domin gina muhalli ko wajen kasuwanci.

Daga bisani Hon.Muhammadd Uba Gurjiya ya ba da tabbacin cewa kwamitin zai rika bibiyar al’amuran kasa domin tabbatar da komai yana gudana bisa tanadin doka kamar yadda sanarwar da sakataren yada labarai na majalisar dokokin jihar Kano, Nura Bala Ajingi ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here