Buhari Ya Caccaki BBC Da CNN Kan rahotansu na EndSARS

0
107

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya kadu da rahotannin da kafofin yada labarai na ketare da suka hada da BBC da CNN suka bayar kan zanga-zangar adawa da cin zalin ‘yan sanda mai taken EndSARS.

Buhari ya bayyana haka ne a yayin wani taro da gwamnonin jihohin kasar a fadarsa da ke birnin Abuja a ranar Talata.

Shugaban ya caccaki BBC da CNN kan yadda suka cire batun kisan da aka yi wa ‘yan sanda da kona ofisoshinsu a rahotanninsu.

“Na kadu da daukar rahotan wanda bai mayar da hankali kan ‘yan sandan da aka kashe da ofisoshinsu da aka kona da kuma gidajen yarin da aka fasa ba” inji Buhari ta bakin mai magana da yawunsa Garba Shehu.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne matasan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar EndSARS a manyan biranen kasar da suka hada da Lagos da Abuja, inda suka bukaci gwamnati ta rusa rundunar ‘yan sandan da ke yaki da ‘yan fashi tare da kawo karshen cin zalin da jami’an ke yi wa jama’a.

Tuni aka rusa wannan runduna tare da kafa wata sabuwa da za ta maye gurbinta biyo bayan kwanaki da fara zanga-zangar.

Sai dai hakan bai dakatar da masu zanga-zangar ba, abin da ya sa sojoji suka bude wuta kan dandazon masu boren a unguwar Lekki da ke jihar Lagos, lamarin da ya yi sanadiyar rikidewar zanga-zangar zuwa tarzoma.

An zargi bata-gari da shiga cikin wannan zanga-zanga domin yi wa al’umma barna ta hanyar farfasa shaguna da bankuna har ma da far wa jami’an tsaro musamman ‘yan sanda kamar yadda sashin Hausa na RFI ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here