Budurwa Ta Kai Ƙarar Saurayinta Kotu Bisa Ɓata Mata Lokaci Bai Aureta Ba

0
273

Wata budurwa a kasar Zambia ta kai karar saurayinta bisa bata mata shekaru takwas suna soyyaya daga karshe kuma bai aureta ba.

Budurwar mai suna Gertrude Ngoma mai shekaru 26, rahotanni sun bayyana cewa ta shaidawa kotu a Zambia cewa saurayinta mai suna Herbert Salaliki mai shekaru 28 ba shi da niyyar aurenta kuma ta gaji da hakurin jiran su zama mata da miji.

Kamar yadda wani mawallafin jarida a kasar Zambia, Mwebantu ya rawaito, Gertrude wacce ke rayuwa tare da iyayenta ta samu yaro da Herbert.

Rahotan ya ce saurayin ya jima da bayar da sadaki amma har yanzu bai auri masoyiyar tashi ba, wacce ta gaji da jira.

“Ba dagaske yake ba, shi yasa na kai shi kotu saboda na chanchanci nasan mafita da kuma rayuwarmu ta gaba”, inji ta.

A nasa martanin, Hebert ya ce yana fama da matsalar kudi ne wanda zai shirya bikinsu kuma ya zargi Ngoma da kin bashi kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here