An Sace Dan Majalisa a Gidansa a Jihar Taraba

0
90

Yan Bindiga sun sace Dan Majalisa mai wakiltar Nguroje a majalisar dokokin jihar Taraba, Barista Bashir Mohammed.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an sace dan majalisar ne daga gidansa wanda yake kusa da ofishin SSS na Jalingo da misalin karfe 1:30 na dare ranar Laraba.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, yan bindigar wadanda sun sun fi su goma da manyan makamai sun kutsa gidan dan majalisar da karfe 1:30 na dare sannan kuma sun ta yin harbi a yankin na tsawon mintuna 45 kafin su sace dan majalisar.

Barista Bashir Mohammed, dai shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Taraba.

Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP David Misal, bai amsa kiran da aka yi masa ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here