An Ɗage Zaman Tattaunawa Tsakanin Gwamnati da Kungiyar ASUU Har Sai Baba-Tagani

0
113

An dage tattaunawa da aka shirya yau tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU.

Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce an dage tattaunawar ne saboda lokacin da aka ba wa kungiyar na tuntubar mambobinta ya yi kadan.

A gefe guda kuma, gwamnatin tarayya ta ce kungiyar ta ASUU ta amince da janye yajin aikin da ta ke yi a yau.

Ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce kungiyar ASUU ta amince da yarjejeniyar ne a taron da suka yi da gwamnati ranar 27 ga watan Nuwamba.

“Maganar gaskiya kan lamarin shi ne an cimma yarjejeniya a zaman da aka yi na karshe wanda kungiyar ASUU ta amince da janye yaki kafin ranar 9 ga watan Disamba, shi ma minista ya amince idan ASUU ta janye yajin aikin, zai samu amincewar fadar shugaban kasa wajen biyan alawus din yan kungiyar kafin 9 ga watan Disamba”, inji Ngige.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here