Yanzu-Yanzu: Jam’iyyar APC ta Kori Hilliard Eta daga Jam’iyyar

0
171

Jam’iyyar APC ta kori tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudu maso kudu, Hilliard Eta.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ne ya bayyana hakan a yau Talata bayan taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Jam’iyyar ta ce an dauki matakin ne bayan Eta yaki janye karar da ya kai jam’iyyar ta APC.

Haka kuma jam’iyyar ta kara wa’adin wata 6 ga kwamitin riko na jam’iyyar.

Sannan jam’iyyar ta rushe shugabancinta tun daga mazabu zuwa jihohi da shiyoyi inda za’a kafa kwamitin riko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here