Ofishin Jakadancin Najeriya a Jamus Ya Kori Ma’aikacinsa Bisa Kamashi da Laifin Lalata da Mata

0
104

Ofishin jakadancin Najeriya a kasar Jamus ya kori daya daga cikin ma’aikantsa wanda ya kasance jami’in tsaro ne bayan an same shi da laifin yin lalata da sauran laifuka.

Jami’in tsaron mai suna Martins Adedeji Oni, an kore shi daga aiki nan take.

Ofishin jakadancin ya bayyana sanarwar korar ne a shafinsa na na Twitter @NigeriaBerlin yau Talata inda ya yi bayanin cewa baza su lamunci duk wani abu na sabawa dokar aiki ba.

Korar ma’aikacin na zuwa ne wata daya bayan wani bidiyo da ya yi yawo a kafafen sadarwa ya nuna ma’aikacin a dakin Hotal ba kaya a rabin jikinsa yana musu da wani mutum wanda ya soke shi da neman yin lalata da matan da suka nemi sabunta fasfo dinsu.

Ofishin jakadancin a bayanan da ya walkafa yau Talata ya ce kwamitin bincike ya samu Oni da laifin da ake zarginshi.

A cewar sanarwar kwamitin ya tattauna da Mista Oni da sauran shaidu inda aka tabbatar da zargin da ake masa a don haka ne ofishin ya sallame shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here