Gwamnatin Jihar Katsina Ta Hana Makarantu Amfani da Groups din WhatsApp

0
122

Gwamnatin jihar Katsina ta bada umarni ga shugabannin makarantun sakandire a jihar da su rufe kowanne group na whatsApp da malamai suke amfani da shi a makarantun gwamnati.

A wata wasika mai dauke da sa hannun Muhammad Sada Dikko a madadin ko’odineta a ma’aikatar ilimi ta jihar ya zargi group na shafukan sadarwa da karfafa giwa wajen tabarbarewar makarantu.

“Ina bada umarni ga dukkan shugabannin makarantun sakandire da su umarci group admins na makarantunsu da su goge groups na whatspp.

” Hana amfani da wannan group din ya zama dole sakamakon wallafa rubuttukan dake haifar da matsala tsakanin makaranta da ma’aikata.

“Shugabannin makaranta kuma su sanar da ma’aikata kan umarnin gwamnati na hana ma’aikata yin magana mai kyau ko mara kyau kan ayyukan gwamnati a shafukan Facebook da WhatsApp”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here