An Zargi Ƴan’uwan Shugaban APC na Kano,Abdullahi Abbas Da Kassara Albashin Wani Ma’aikaci

0
248

Wani ma’aikaci a karamar hukumar birnin Kano, mai suna Khalifa Mukhtar, ya koka kan dakatar da albashinsa bisa kin ci gaba da bawa Arifi Abbas dan’uwa ga shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas wani Kaso cikin albashin nasa.

Khalifa Mukhtar ya shaidawa jaridar Sahelian Times yadda Amina Abbas, Daraktan tafi da ayyuka na Musamman a karamar hukumar Nasarawa(DPM) da Arifi Abbas R.O a karamar hukumar Fagge; dukkanninsu yan uwa ga Abdullahi Abbas, suka hada baki wajen kassara albashin da yake dauka.

“Arif Abbas ya bani takardar daukar aiki a shekarar 2011. Bayan haka ya bukace ni mu dinga raba albashin tare da shi”, inji Mukhtar.

“Na shafe shekaru 9 ina biyansa dubu 9 duk wata daga cikin albashina, da kuma karin shekaru 4 ina biyansa dubu 7 duk wata wanda ya kai shekaru 11”, inji shi.

Haka kuma, bayan gajiya da bashi wani kaso na albashinsa wanda ya ce ya bawa Arifi Abbas kusan Naira Miliyan 1 cikin shekaru 11, sai yaki ci gaba da bada wannan kudi.

“Saboda daga karshe na yanke hukuncin dena biyansa, sai ya hada kai da yar uwarsa, Hajiya Umma Abbas inda suke zarar kudi daga albashina”.

“Yayin da na karbi albashina na watan Satumba, sai naga babu dubu 35, 000. Yayin da na tuntuba sai aka fada min cewa na karbi bashin kudi dubu dari uku, sannan wannan cire kudin da aka yi daga albashina umarni ne daga Umma Abbas”, inji shi.

Mutumin ya shigar da korafi ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, kodayake ya yi zargin cewa maimakon ya samu adalci, sai Arifi da Amina suka hada kai wajen sanya karamar hukumar birni ta dakatar da biyansa albashinsa gabadaya.

Ana ta bangaren, Umma Abbas ta shaidawa jaridar Sahelian Times cewa, baza ta ce komai kan wannan batu ba, inda tayi ikirarin cewa ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta kafa kwamiti don bincike kan lamarin.

Jaridar ta Sahelian Times ta rawaito cewa ta yi yunkurin tuntubar Arifi Abbas da DPM na karamar hukumar birni amma abun ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here