Ƴan Kasuwar Sabon Gari Sun Nemi Ɗaukin Majalisar Dokokin Jihar Kano

0
515

 

Gamayyar ƙungiyoyin ƴan kasuwa na kasuwar Mohammed Abubakar Rimi dake Sabon Gari sun nemi majalisar dokoki ta jahar kano ta yi duba na tsanaki akan wata doka dake gabanta akan kasuwar wacce suka ce za ta kassara harkokinsu na kasuwanci.

Da yake jawabi ga shugaban majalisar dokokin jahar kano akan batun, Shugaban kungiyar ƴan kasuwar Alh. Ali Bagadaza ya ce hakika dokar za ta kawo koma baya a harkokin ‘yan kasuwa da dama.

Ya kuma bayyana rashin gamsuwarsa akan jagorancin shugaban kasuwar Alh. Uba Zubairu Yakasai inda ya ce zuwansa a matsayin shugaba a kasuwar ya haifar da lalacewar harkokin kasuwancinsu.

A nasa jawabin shugaban majalisar Rt. Hon. Abdul’azeez Garba Gafasa ya ce majalisar za ta tuntubi dukkanin wadanda dokar ta shafa domin tabbatar da ganin an yiwa kowanne bangare adalci.

Walin Gaya ya bayyana cewa majalisar za ta yi duk wani yunkuri da zai Samar da zaman lafiya da bunkasa harkokin ‘yan kasuwar.

Shugaban majlisar Wanda ya nuna gamsuwa da halin da’a da bin matakin da ya dace wajen shigar da kokensu ya kuma ba su tabbacin cewa majalisar za ta yi kokarin ganin dokar ta zama masalaha ga ‘yan kasuwar kafin su yi doka akanta kamar yadda sanarwar da sakataren yaɗa labarai na majalisar Nura Bala Ajingi ya fitar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here