Jam’iyyar ADC ta Nisanta Kanta daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Kano

0
143

Jam’iyyar ADC ta nisanta kanta daga shiga zaben kananan hukumomi wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta shirya a watan Janairu mai kamawa.

Sannan jam’iyyar ta yi barazanar kai karar hukumar zaben ta Kano idan har ta sanya sunanta da tambarinta a takardar zabe.

Shugaban jam’iyyar ta ADC, Comrade Musa Shuaibu Ungogo ne ya bayyana hakan a karshen wannan makon yayin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce hukumar zaben ta KANSIEC ba ta tuntubi jam’iyyar ADC ba kan shirye-shiryen zaben kuma jam’iyyar baza ta shiga zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli ba.

Ya ce, jam’iyyar tunda farko ta bayyana matsayarta kan lamarin wanda ya ce shi ne baza ta shiga zaben ba.

“Kamar al’amara, mu ka ga sunanmu cikin jerin sunayen mutane 42 daga jam’iyya suna neman takarar shugabannin kananan hukumomi da mutane 400 suna neman matsayin Kansila,” inji shi.

ADC ba ta fitar da wani jerin sunaye ba don haka ya zama dole mu yi kira ga hukumar zabe kan ta cire sunanmu da na yan takara daga takardar zabe.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here