Ba za Mu Amince Da Zanga-Zangar EndSARS ba – Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya

0
525

Sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya ta NANS, Sunday Asefon, ya yi Allah-Wadai da zangar-zangar #EndSARS, wacce matasa suka gudanar a kwanakin baya.

Asefon ya ce zanga-zangar EndSARS ba za ta shawo kan matsalar cin zarafin da yan sanda ke yi ba saboda babban sufeton yan sanda na kasa ya rushe rundunar ta SARS.

A watan Oktoba ne dai, matasa a kasarnan suka fantsama kan tituna suna adawa da rundunar ta SARS.

Sai dai daga baya yan daba sun yi amfani da zanga-zangar wajen sace dukiyoyin al’umma.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja shugaban kungiyar daliban ya ce kungiyar ba ta amince da zanga-zangar #EndSARS ba saboda ba ta da shugaba.

Asefon ya kuma ce kungiyar Daliban za ta tattauna da gwamnati da kuma kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU don ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here