Zaɓen Cike Gurbi: An Sace Ma’aikatan Wucin Gadi na INEC a Jihar Zamfara

 

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun bayayana cewa an sace wasu ma’aikatan wucin-gadi biyu na Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

Su dai wadannan Ma’aikatan na INEC an sace su ne a jiya Asabar bayan kammala zaben cike gurbi na dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Bakura.

Baturen Zaben Cike gurbin, Farfesa Ibrahim Magawata ne ya bayyana batun Sace wadannan ma’aikata a yau Lahadi.

Farfesan ya kuma ayyana zaben a Matsayin wanda bai kammala ba sakamakon wasu matsaloli da aka samu.

Kafin ayyana zaben a Matsayin wanda bai kammala ba dai, dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Tudu ne kan gaba da yawan kuri’u 18,645, yayin da dan takarar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji ke da kuri’u 16,464.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here