Yadda na Haihu a Bakin Kofar Asibitin Nuhu Bamali Kano – Wata Mata

0
260

Wata Mata mazauniyar unguwar sheka sabuwar Abuja dake Kano, ta bayyanan wa jaridar Prime Tmes yadda ta haifi ‘yarta a bakin kofar Asibiti Nuhu Bamali dake birnin Kano.

“A ranar Sha bakwai ga watan nuwamba na shekara 2020 Wanda yayi daidai da ranar Talata da misalin karfe 11:00 na dare muka Isa bakin asibitin Nuhu Bamali dake jahar Kano,domin tun a hanya ji nake kamar zan haihu a cikin adaidaita sahu Amma da muka Isa bakin asibitin na Nuhu Bamali,sun rufe duk da irin buga kofar da mukayi don a bude Mana tare da kawo Mana dauki sai da muka shafe kusan sa’a guda amma basu bude ba, nan take na haihu agurin,A haka aka samu aka
lulube yar da zani ba tare da mahaifar ta fito ba tsabar sanyi.

 

“Ko da yake yar tayi kuka sau Daya Amma bata Kara ba,sai a lokacin da daya daga cikin malaman jinyar ta taso daga bacci ta fara mita,wai mai yasa muka zo a cikin daren nan?,  Kuma sai dai mu gyara gurin da na haihu yayin da dayar Kuma raino yar ta takeyi.

“Bayan da mahaifa ta fito suka saka yar a sikeli,sai suka ce ai lafiyata kalau,Amma a daren da muka dawo gida da misalin karfe 1 na dare,numfashin yar Yana sarkewa,hancita Yana toshewa ,sai dai tayi nunfashi ta baki.

“Washe gari na kai yarinyar asibiti murtala dake Kano bayan gwaje -gwaje da akayi mana da tambayoyi sai suka tabbatar min da cewa ya ta sanyin gurin ne ya shige ta, bayan kwana Daya da dawowa ta rasu., ” Inji matar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here