2023: Malaman Kano Sun Musanta Goyan Bayan Takarar Tinubu

0
136

Majalisar malamai ta Kano ta karyata batun cewa ta goyi da bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu a takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Shugaban majalisar malaman, Malam Ibrahim Khalil ne ya musanta batun yayin da yake zantawa da manema labarai yau a Kano.

Idan za’a iya tunawa dai, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Kano a ranar Juma’a inda ya halarci daurin auren yar gidan Sheikh Muhammad Bn Usman.

Malam Ibrahim Khalil, wanda ya bayyana mamakinsa kan yadda kafafen yada labarai suka rawaito cewa sun goyi da bayan Tinubu ya ce irin wannan labari zai haifar da rashin jituwa tsakanin malamai.

Ya ce “Bola Tinubu ya zo Kano don halartar daurin Auren yar gidan Sheikh Muhammad Bn Usman, magobayan Buhari sun yi taron siyasa a Gidan Mambayya sannan ya karbi bakuncin wasu kungiyoyin musulmai dake fadin Najeriya sannan Oba na Legas ma ya kai masa ziyara bayan zanga-zangar EndSARS a Legas bisa rasa rayuka da dukiyoyi”.

Malamin ya ce bai kamata ace malaman Kano sun goy da bayan takarar Tunubu ba saboda suna da banbancin ra’ayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here