Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Wata 6 Ga Wanda ya yi wa Yar shekara 14 Fyade

0
253

 

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Kotu ta tura Emmanuel Thompson Udo gidan gyara halin wato kurkuku tsawon wata shida sakamakon zarginsa da Kuma samunsa da laifin aikata wa ‘Yar Goyon sa Mai shekara 14 da Haihuwa fyade (an sakaya sunan yarinyar).

Ko a kwanan Baya ma an samu Wani jami’in gwamnatin jahar Kuros Riba da laifin aikata fyade.

A Najeriya kwanan Baya lokacin da akayi kullen cutar kurona ana yawaita samun karuwar aikata fyade.

Da yake tabbatar da haka ga manema labarai shugaban kungiyar Kare hakkin dan Adam wato Basic Right Council initiative a turance Barista James Ibor ya tabbatar da cewa Babban mukaddashin alkalin kotun sasanta iyalai Mai shari’a E.E.Ita ne ya yanke hukuncin tura Thompson Udo zuwa gidan gyara halin.

Daga nan ya godewa Hukumar Yan sanda da ta gabatar da kararraki da Tanko Ashang,da Kuma Felix Itittam dama Blessing Egwu saboda tsayiwar daka da sukayi wajen yanke hukuncin tura Thompson kurkuku.

Ya ce shari’a ta yi adalci idan ana samun hukunta masu Hali irin wancan yana Zama izna ga na Baya za’a samu raguwar aikata fyade a jahar Kuros riba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here