Jonathan Ya yi Bayani Kan Batun Takarar Shugaban Kasa a Shekarar 2023

0
235

 

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce lokaci bai yi ba da zai yanke hukunci ko zai tsaya takarar zaben shekarar 2023 ko kuma a’a.

 

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da makomar siyasar sa a shekarar 2023,Jonathan yace lokaci bai yi ba da zai yi magana a kai.

Ziyarar da wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka kaiwa tsohon Shugaban lokacin da ya cika shekaru 63 da haihuwa ta haifar da ce-ce kuce dangane da makomar siyasar sa da kuma takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023,inda wasu ke hasashen cewar Jonathan zai koma APC domin tsayawa takarar zaben.

Dangane da matsalar tsaron da ya addabi Najeriya,tsohon Shugaban ya ce ba shida hurumin magana a kai,domin koda yake mulki ya fuskanci irin wadannan matsaloli.

Jonathan ya ce abin yi yanzu shine goyawa gwamnati baya da karfafawa sojoji da sauran jami’an tsaro gwuiwa domin kara kaimi wajen shawo kan matsalar.

Tsohon Shugaban ya ce matsalar tsaro yau ta zama ruwan dare game Duniya,saboda haka ya dace a janyo hankalin matasa wajen amfani da fasahar da Allah ya basu domin hada kan jama’ar kasar ga baki daya kamar yadda sashin Hausa na RFI ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here