Kotu Ta Bada Umarnin a Tsare Abdulrashid Maina a gidan Gyaren Hali Har zuwa Lokacin da za a Kammala Shari’ar da ake yi masa

0
118

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja a yau Juma’a ta bada umarnin garkame Abdulrashid Maina tsohon shugaban kwamitin asusun yan fansho a gidan gyaran hali har zuwa karshen kammala shari’ar da ake yi masa.

Mai shari’a Okon Abang ne ya sanar da hukuncin bayan bukatar da lauyan hukumar EFCC, Barista Mohammed Abubakar ya shigar.

Maina wanda hukumar EFCC ke tuhumarsa da badakalar kudi har Naira Biliyan 2 ya guda zuwa kasar Nijar bayan belinsa da aka bayar tunda farko.

Sai dai an samu nasarar taso keyarsa zuwa Najeriya a jiya Alhamis.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here