Jami’ar East Corolina dake Amurka Ta Musanta Batun Ba wa Ganduje Mukamin Farfesa

0
184

Jami’ar Amurka ta musanta batun cewa ta nada gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Farfesa.

Jami’ar East Carolina(ECU) ta ce wasikar da Ganduje ya samu daga wani mamba na tsangayar jami’ar hukumar ba ta san da ita ba.

Jami’ar ta yi bayanin matsayarta ne a wata wasika da ta aikawa gwamnan Kano wacce kuma jami’ar ta aikawa jaridar PREMIUM TIMES.

Tunda farko dai, sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa nadin gwamnan na dauke ne cikin wata wasika da jami’ar ta aiko masa ta hanyar daya daga cikin malamanta, Victor Mbarika.

Jami’ar ta tabbatar da cewa Mista Mbarika na daya daga cikin ma’aikatanta amma bashi da hurumin yin irin wannan nadin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here