Gwamna Zulum Ya Raba Tallafin Dubu Dari 6 Ga Kowanne daya daga Iyalan Manoman da aka Kashe

0
167

Gwamnatin jihar Barno ta raba tallafin kudi Naira Dubu dari 6 ga kowanne daya daga iyalan manoma 48 da ake kashe a jihar.

An kuma ba wa iyalan mamatan buhunan kayan abinci wanda kwamitin da gwamna Baba Zulum ya kafa ya bayar ga iyalan.

Kudin da aka raba sun samu ne daga tallafin da kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta bayar na Naira Miliyan 20 da kuma Naira Miliyan 5 da hukumar bunkasa ci gaban yankin arewa maso gabas ta bayar.

Kwamitin karkashin shugabancin kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Saina Buba, ya kai kayan tallafin zuwa Zabarmari a a jiya Alhamis.

Akwai buhun shinkafa dubu 13 da na masara da wake 1, 300 da man girki 2116 da kwalin maggi da tumatirin leda 1,083 buhun gishiri 650 wanda ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta raba.

Kwamishin ya ce kowanne iyali an bashi Naira dubu dari 6 da kayan abinci don rage musu radadin da suke ciki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here