‘Da ni Za’a Rushe Ginin Kadarorin Gwamnati da Ganduje Ya Siyar’ – Kwankwaso

0
2445

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jagoran Darikar Kwankwasiyya, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya sha alwashin rushe duk wani gini na kadarorin jihar Kano da gwamnatin Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta siyar da zarar jam’iyyarsa ta lashe zaben gwamna a shekarar 2023.

Kwankwaso na bayanin hakan ne cikin wani shiri na musamman da aka sanya a gidan Rediyon Nasara dake Kano a daren jiya Alhamis.

Tun da farko dai, tsohon gwamnan ya bayyana dalilansu na kin shiga zaben kananan hukumomi dake karatowa, inda ya ce bayan “shawara da uwar jam’iyya ta kasa” sun yanke shawarar kaucewa shiga zaben.

Sannan Sanata, Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan yadda ya yi zargin gwamnatin jihar na ciyo bashi.

Sannan ya yi batun kan halin rashin tsaro da ake fuskanta a yankin Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here