Shekarau Ya Caccaki Buhari Kan Ƙin Sauke Manyan Hafsoshin Tsaro

0
521

Sanata Ibrahim Shekarau ya ce shugaban kasa Muhammadu ya na karya doka bisa ci gaba da barin manyan hafsoshin tsaron kasarnan kan kujerarsu.

Biyo bayan kisan gillar da aka yi a garin Koshebe na jihar Barno, yan Najeriya da dama sun yi kira da a sauke manyan hafsoshin tsaro, inda suka ce sun gaza.

Shekarau wanda ya kasance bako a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin din Channels ya ce Dangane da muhawarar da ake kan kokari, manyan hafsoshin tsaron kasarnan sun kammala shekarunsu na aiki don haka an karya dokar tafi da aiki na barinsu.

“Shugaban kasa na karyar doka, doka cewa ta yi idan shekarunka suka kai 60 dole ne ka ajiye aiki.

“Idan ka shekara 35 kana aiki, dole ne ka ajiye aiki, a takaice ma su ba ma’aikatan shugaban kasa ba ne, su ma’aikatan Najeriya ne kuma akwai doka, ” ini Shekarau.

tsohon gwamnan na Kano ya ce babu daya daga cikin manyan hafsoshin da ya yi aiki kasa da shekara 35 lamarin da ya sa yakamata su yi ritaya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here