Rikicin APC: Tsagin Jam’iyyar a Kano Ya Rushe Shugabancin Abdullahi Abbas

0
935

Tsagin jam’iyyar APC karkashin shugabancin Hussaini Isa Mai Riga, ya rushe shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Abdullahi Abbas.

An sake zabar shugabancin Abdullahi Abbas ne a watan Mayu na shekarar 2018 bayan rikicin da ya faru a jam’iyyar a shekarar 2017.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano yau Alhamis, Mai Riga ya yi zargin cewa zaben da aka ayyan tsagin Abdullahi Abbas a matsayin shugaba an yi shi ne ba bisa ka’ida ba kuma sun gaza wajen hade kan jam’iyyar.

“Abinda yake a gaskiya shi ne shugabancin Abdullahi Abbas ya saba da dokar jam’iyya don haka duk abin da zai zo daga bangaren ya zama haramtacce”.

Mai riga ya bukaci yan jam’iyyar dake yin takara a zaben kananan hukumomi da za’a yi a jihar karkashin shugabancin Abdullahi Abbas, a kan kar su bata lokacin su inda ya ya ce za’a ayyana zaben a matsayin haramtacce.

“Abinda nake nufi shi ne duk wanda yake takara a zaben watan Janairu na shekarar 2021 karkashin shugabancin Abdullahi Abbas kamar ya na bata lokacinsa ne saboda koda yaci zabe. Zaben ya haramta” inji shi.

“Idan ka lura ko yadda aka fitar da yan takarar shugabancin kananan hukumomi zaka ga an sabawa dimukuradiyya, saboda an hana a siyar da form din takara ga kowa sai wanda suke so.”

Mai Riga ya kuma yi kira ga uwar jam’iyyar ta kasa da ta kafa kwamitin riko da zai jagoranci zaben kananan hukumomin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here