An Kashe Mataimakin Kwamishinan Yan sanda a Jihar Kuros Riba.

0
78

 

Daga Musa Muhammad Kutama Kalaba

Wasu da ba’a san ko suwaye ba da ake kyautata zaton Yan fashi da makami ne sun kashe mataimakin kwamishinan Yan sanda (ACP) Mai Suna Egbe Eko Edum a unguwar Ikot Effanga Daura da Babbar hanyar shiga Kalaba sakamakon Hari da suka kai Masa da Adda.

Eko Edum shine kwamandan rundunar Yan sandan bataliya ta 73 ta Yan sandan kwantar da tarzo wato PME dake Magumeri ,jihar Borno.

Ya baro can ne zuwa Kalaba da nufin yazo yaga iyalansa wajen karfe daya na dare mota ta sauke su shida abokinsa Lauya barayin suka far musu.

Wani makwancin kwamishinan Mai suna Ekong ya shaidawa manema labarai a Kalaba cewa barayin mamaye su sukayi suka bukaci Sai su mika musu wayoyin hannunsu da jakunkunan su na tafiya shi lauyan ya mika nasa yayin da Edum Kuma ya tsaya yin jayayya da barayin suka sassareshi da Adda har ya kai ga ajalinsa.

DSP Irene Ugbo kakakin rundunar’Yan sandan jihar Kuros Riba ta gaskata faruwar hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here