Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Za mu Horar da Jami’an Yaɗa Labarai – KANSIEC

0
207

 

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Shugaban Hukumar zabe Mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSEIC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka, ya ce zasu Bayar da Bita ta musamman ga Jami’an yada Labarai na Kanan Hukumomin jihar Domin Samun Damar yada ingantattun labarai kamar yadda ya kamata.

Sheka Ya Bayyana Hakane sa’ilin da yake Karbar wasu daga cikin Shuwagananin na Jami’an inda yace ko shakka Babu Hukumarsa za ta yi Duk mai yuwuwa wajen Ganin ta Basu Duk wata Gudunmawar da Zata Basu Damar Gudanar da aikinsu a yayin Zaben Kanannan Hukumomin dake Gabatowa.

Da yake nasa Jawabin a Madadin daukacin Jami’an Sagiru Abdullahi kwanar Gora wanda ke a matsayin Shugaba ga Jami’an yada labaran na Kanannan Hukumomi ya Bayyana godiyarsa ga Hukumar zabe jihar tare da Tabbatar da cewa Zasu tsaya da gaskiya tare da Rikon Amana Wajen Bayyana Gaskiyar Abinda ke Faruwa a yayin Zaben Kanan Hukumomin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here