Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Amince Zai Bayyana Gaban Majalisar Wakilai Ta Kasa Don yin Bayani Kan Matsalar Tsaro

0
129

Shugaban majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince zai bayyana gaban majalisar don yi musu bayani kan kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasarnan.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Talata ne majalisar ta amince da kudurin gayyato shugaban kasar don yin bayani kan matsalar tsaro da ake fuskanta a kasarnan.

Yayin da yake jawabi ga wakilan kafafen yada labarai na fadar gwamnatin tarayya, shugaban majalisar wakilan ya ce shugaba Buhari zai girmama gayyatar ta su.

Ya ce za’a sanar da ranar da shugaban kasar zai je majalisar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here