Matasan Masarautar Ofutop da ke Yankin Niger Delta Sun Bankawa Sarakunansu Wuta

0
142

Daga Musa Kutama , Kalaba

Matasan masarautar Ofutop dake yankin Karamar hukumar Ikom Jahar Kuros Riba dake yankin Niger Delta sun tattara sarakunan su sun banka masu wuta da kyar da jibin goshi sarakunan suka tsira.

Majiya daga masarautar ta shaidawa Wakilin mu cewa matasan sun gayyato sarakunan ne yayinda suke dakunan iyalansa Suna barci da misalin karfe 11 na dare suka kaisu Dandalin da mutanen kauyukan kanyi taro kowace shekara domin tattauna matsalolin da suka shafesu ashe matasan sun tanaji manfetur suka bulbulawa sarakunan nan take suka kyasta ashana suka jefa masu wuta ta kamasu.

Majiyar taci gaba da shaidawa Wakilin mu cewa matasan sun kona basarake Emuru Shima Mai Suna Ntun Ayan Ekum Shima ya Sha da kyar.

Matasan sun zargi sarakunan ne da yin sakaci na rashin daukar matakin mutuwa da galibin matasan masarautar keyi ne Babu gaira ba dalili.

Mutuwa ta Wani matashi a yankin Mai Suna Osim Ebuk Obim kazalika Suma matasan kauyen Isiele sunyi yunkurin kona nasu sarkin.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kuros Riba DSP Irene Ugbo ta shidawa wakilin mu su na nan Suna bincike Amma Basu kai ga kama kowa ba idan Hali yayi zata sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here