Gwamnonin Arewa Sun Goyi bayan Gayyato Sojojin Haya

0
241

 

Gwamnonin jihohin dake arewa maso gabashin Najeriya sun goyi bayan kiraye kirayen da ake yiwa gwamnatin tarayyar na dauko sojojin haya domin murkushe mayakan Boko Haram da suka addabi yankinsu.

Gwamnan jihar Taraba darius Ishaku ne ya bayyana matsayin gwamnonin arewa maso gabashin Najeriyar a ranar talata, lokacin da suka ziyarci takwaransu na Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, don jajanta kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma da dama a karamar hukumar Jere.

Gwamnonin sun ce dari bisa dari sun goyi bayan jerin bukatu ko shawarwarin da gwamnan Borno ya mikawa gwamnatin tarayyar Najeriya kan murkushe kungiyar Boko Haram, wanda cikinsu har da dauko sojojin haya.

Baya ga gayyato sojojin haya, gwamnan Borno ya kuma bukaci daukar karin dubban matasa aikin soja, musamman daga cikin ‘yan Civilian JTF da suak shafe shekaru suna taimakawa dakarun Najeriya wajen yakar Boko Haram.

Sauran bukatun da gwamnan ya mika sun hada da sayan motocin yaki masu sulke da isassun makamai da za su taimakawa sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen samun nasarar murkushe kungiyar Boko Haram kamar yadda sashin Hausa na RFI ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here