Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattijai Ta Bukaci Buhari Ya Sauke Manyan Hafsoshin Tsaro

0
128

Majalisa dattajai ta bukaci shugaban kasa Buhari da ya kori “Dadaddun” manyan hafsoshin tsaron kasarnan.

Majalisar ta yi kiran ne bayan kudurin da Sanata mai wakiltar Barno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya gabatar.

Kiran na majalisar na zuwa ne watanni 6 bayan sun bukaci manyan hafsoshin tsaron kasarnan da su yi murabus.

Manyan hafsoshin dai da wa’adinsu na yin ritaya ya cika sun hada da Gabriel Olanisakin, babban Hafsan tsaron kasa, Tukur Burutai, babban hafsan Soji, Sadique Abubakar, Babban Hafsan sojin sama da Ibok-Ete Ekwe Ibas babban Hafsan sojin ruwa.

Kashim Shettima ya ja hankalin majalisar kan kisa manoma 45 a garin Kwashabe na jihar Barno.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here