Wata Mata ta yi wa Mahaifiyarta Yankan Rago a Jihar Akwa Ibom

0
90

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Wata mata da Yan sanda suka kamata a Garin Ikot Ekpene jihar Akwa Ibom Mai Suna Mary Imewe da ta yiwa mahaifiyarta yankan Rago ta shaidawa Yan sanda cewa idan Suna da gari na Lahira ba don ta yanka mahaifiyar ta ba su kaita.

Mary wadda ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa ta shaidawa Yan sanda cewa mahaifiyar Tata ta hana mata yin arziki Tana yawan Sanya mata Ido shi ya Sanya ta dauki matakin yi mata yankan Rago.

Dattawan unguwa sun umarci Iweme da ta zuba Gunduwa-gunduwar gawar a masaki a zagaya da ita unguwa kowa ya ganta yaga abinda ta aikata.

Wadda ake zargin tayi furucin ita ta yanka mahaifiyarta ta don haka mutane Babu ruwan su a fita sha’aninta.

SP Odiko Macdon Mai magana da yawun rundunar Yan sandan jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa manema labarai afkuwar Hakan yace “Tabbas labarin da gaske ne ga wadda ake zargin ana tsare da ita,  inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here