Na samu Nasarori Amma Babban kalubale na shine na tsaro -Injiniya Abdullahi Kutama

0
99

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

 

Shugaban Karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya Fadi a ganawar da yayi da manema labarai a ofishin sa cewa mutane har yanzu wasu sun kasa fahimtar manufofin Gwamnati.

Shugaban Wanda halin yanzu jamiyyar sa ta APC ta duba cancantar akwai bukatar ta sake Bashi dama yayi ta Mike wa’adi na biyu a shugabanci Karamar hukumar Gwarzo ya ci gaba da zayyana dimbin Nasarori da ya samu cikin shekara uku da yayi na wa’adi mulkinsa da suka hada da “Gyara masallatan juma’a guda 50 samarwa matasa ayyukan yi gyara wasu daga cikin hanyoyi na mota a wasu garurukan dake mazabu goma na wannan Karamar hukuma”.

Injiniya Abdullahi Kutama yaci gaba da cewa Duk da yake lokacin da ya karbi jagorancin Karamar hukumar Gwarzo ya tarar da dimbin matsaloli da take fama dasu “Amma cikin ikon Allah da ludufinsa yayi mana jagora mukaci gaba da ayyukan raya Karamar hukumar Gwarzo “.

Wannan kwazo na shugaban Karamar hukumar Gwarzo ya cikin Wani yanayi da kullen kurona ya jawo Amma Duk da haka anyi ayyuka a garurukan Getso,Lakwaya ,Mainuka ,Gadar Fada” wadda gwamnatin tarayya ce yayi ta ta lalace muka gyra”, Inji shi.

Kazalika shugaban karamar hukumar Gwarzo yaci gaba da cewa “mun Samar da ruwan famfo a garurukan Kutama Gwarzo sannan muna aiki na gyara Babbar magudanar ruwa ta Garin Gwarzo da ayyukan raya Karamar hukuma masu yawan gaske”.

Babban kubalena shine “na tsaro Duk yammacin jihar kano Gwarzo tsohuwar Karamar hukuma ce Mai yawan jama’a Kuma tayi Isyaka da jihar katsina wato ta Karamar hukumar Malumfashi Kuma Babbar hanyar data ratsa ta cikin hedkwatar Karamar hukuma Gwarzo itace take hada jihar kano wannan Karamar hukuma da Jihohin katsina da Zamfara “Don haka zamu ci gaba da tsare al’ummar wannan Karamar hukuma a matakin tsaron ma da na dauka na bude ofishin Dss Frsc, Da na sibil difens kullum muna kara jajircewa wajen karawa da ci gaba da na mutanen mu tsaro”.

Karshe ya jaddada aniyar yin wasu ayyukan raya Karamar hukumar idan Allah ya Bashi dama yin wa’adi na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here